Hukumar FBI Da Ma'aikatar Shari'a Sun Fara Bincike Kan Hari Da Aka Kai Masu Adawa Da 'Yan Wariya.

Dansandan a jahar Virginia yake gadi inda aka kai hari da mota kan masu zanga zanga.

Tuni 'Yansanda suka kama matukin motar dan shekaru 20 da haifuwa daga jahar Ohio.

Hukumar FBI mai binciken manyan laifuffuka,da sashen kare 'yancin Bil'Adama a ma'aikatar shari'a, da kuma ofishin lauyan gwanatin tarayya sun fara bincike kan harin da aka kai da mota kan masu zanga zangar adawa da masu nuna wariya. Lamarin ya auku ne a birnin Charlottsville dake Virginia, makwabciyar nan birninWashington DC.

'Yansanda a jahar suka ce sun kama matukin motar, dan shekaru 20 da haifuwa mai suna James Alex Fields daga jahar Ohio.

Tuni Gwamnan Jahar Terry Mcauliffe, wanda yayi Allah wadai da zanga-zangar da 'yan wariyar launin fatar suka shirya wanda ya zama tarzoma har ya kai ga kisan mutane uku, ya ayyana dokar ta baci, bayan da fada ya barke tsakanin 'yan wariyar da kuma masu adawa da su.

Gwamnan ya fada a shafin Twitter cewa, take-take da kalamai da suka wakana a Charlottsville cikin sa'o'i 24, abu ne da ba za'a lamunta da su ba. Yace 'yancin magana, ba 'yanci bane na tada tarzoma.

Shima da yake magana shugaban Amurka Donald Trump, yayi tur da abunda ya kira "mummunar nuna kyama da gaba hade da tarzoma daga bangarori daban daban.


Sa'o'i bayan da aka soke zanga-zangar, rundunar 'Yansanda ta jahar ta bada rahoton jirginta mai sakar ungulu yayi hadari,kuma jami'anta biyu da suke ciki sun mutu.