Hukumar CISA Tace Ba Za A Iya Yin Katsalanda A Zaben Shugaban Kasa Ba

Yan takarar shugaban kasar Amurka, Donald Trump da Kamala Harris

Hukumar CISA tace, a yanzu ya zama tilas ga kasashen dake son yin katsalandan ga zaben Amurka na ranar Talatan nan, su koma dogara da fayafayan bidiyon karya, da wasu kafafen yada labaran karya, domin kuwa ba yadda za su iya kutsawa ga gurbata sahihin sakamakon zaben.

A yanzu ya zama tilas ga kasashen dake son yin katsalandan ga zaben Amurka na ranar Talatan nan, su koma dogara da fayafayan videon karya, da wasu kafafen yada labaran karya, domin kuwa ba yadda za su iya kutsawa ga gurbata sahihin sakamakon zaben, cewar nazarin baya bayan nan na hukumar kula da samar da tsaro ga zaben Amurka.

Jami’an hukumar samar da tsaron yanar gizo da wuraren tsaro ko CISA , ta fada a ranar Litinin cewa, a kasa da sa’oi 24 kafin a fara kada kuri’a a ranar zabe, babu wata hujja dake nuna alamar akwai wasu makiyan kasashen, irin su Rasha, Iran da China dake da wata kafar da zata bi wajen yin illa ga zaben kasar.

Shugaban hukuar ta CISA Jen Easterly, yace, zai iya bugun gaba cewa, yayi imanin babu wata hanyar da za’a iya bi wajen haifar da cikas kan zabubbukan mu ta yadda har zaiyi wani tasiri kan zaben shuagabn kasar.

Easterly ya shaidawa manema labarai cewa, ganin irin gagarumin tsaron da aka samar iri dabam dabam, da ingancin da aka tabbatar a gwajin da aka gudanar kafin lokacin zaben, zaiyi wuya duk wani mai mugun nufi ya iya keda haddin tsarin gudanar da zabubbukan mu ta yadda har zaiyi tasiri ga sakamakon zaben shugaban kasar ba tare da an bankado ba.

An dai samu kwarin nguiwa daga yadda aka rarraba sha’anin gudanar da zaben na Amurka, yadda ko wacce jiha ke amfani da irin nata tsarin, da tsarin yadda kowanne zai tattara, da daidaita kuri’un da aka kada. Duk da cewa, hakan ya samu ne ta shekarun da hukumar CISA ta kwashe tana shiryawa, ta yin aiki da jami’an zaben jiha dana kananan hukumomi a fadin Amurka.

Irin wannan kokarin na hukumar CISA ya hada da sama da duba tsarin tsaron yanar gizo sama da 700 da daruruwan gwaje gwajen zaben da bayar da horo tun a farkon shekarar 2023.

Bugu da kari, babu wani tsarin gudanar da zabe a jiha dake hade da yanar gizo, kuma kiyasin kashi 97% daga cikin dari na masu kada kuri’a zasu kada kuri’a ne a yankunan su kawai, su kuma gabatar da takardar dake dauke da shedar hakan a matsayin kariya.

Easterly yace,’ ba a taba samun wani lokaci da tsarin gudanar da zabubbukan mu ya samu kariya irin wannan ba. Masu alhakin gudanar da zabe basu taba kasancewa cikin nshiri gudanar da ingantacce kuma tsabtataccen zabe ba kamar a wannan karon.

Ya zuwa ranar Litinin, CISA ta kiyasta sama da Amurkawa milyan 77 tuni sun kada kuri’ar su a yayin zaben wuri, yayin da ake sa ran wasu daruruwan milyoyi zasu fita kada kuri’ar su a ranar zabe.