Hukumar CENI Ta Nijer Ta Hada Hannu Da Kamfanin Gemalto Don Shirin Babban Zabe

A jamhuriyar Nijer an cimma yarjejeniya a tsakanin hukumar zaben kasar da  kamfanin Gemalto na kasar Faransa wace a karkashinta  kamfanin zai hada kundin rajistar zabe irin na zamani akan biliyon 19.6 na cfa. aikin da ake saran kammalawa nan da watanni 16 masu zuwa.

Shugaban hukumar zaben kasar Nijer Mr. Issaka Sounna ya fadi albarkacin bakinsa yayin bukin rattaba hannu akan takardun dake tabbatar da bayarda kwangilar hada kundin rajistar zabe irin na zamani. Kamfanin Gemalto, malakar kasar Faransa ne yayi nasarar samun wannan kwangilar bayan tankade da rairayar takardun kamfanoni kimanin 18 da suka nuna sha’awar samun wannan aikin da zai lakume miliyan 30 na dalar Amurka, wato biliyan 19.6 na cfa, kuma a cewar kakakin Hukumar ta CENI Nafiou Wada, a bisa cancanta ne suka zabi Gemalto domin gudanar da wannan aiki.

Wakilin kamfanin Gemalto Jean Michel Dovieb ya nuna farin ciki da samun wannan kwangilar kuma ya tabbatar da cewa zasu dauki dukkan matakan da zasu bada damar samun nasarar aikin da aka basu.

Akan idon Wasu daga cikin ‘yan siayasa na bangaren jam’iya mai mulki ne aka rattaba hannu akan wannan yarjejeniya

Tsarin jadawalin hukumar CENI ya yi nunin cewa a watan mayun shekarar 2020 ne za a gudanar da zaben kananan hukumomi yayinda ake saran kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a farkon shekarar 2021, sai dai kawo yanzu ‘yan adawa na ci gaba da kauracewa ayyukan na hukumar zabe saboda a cewarsu haramtaciyya ce sakamakon zargin rashin aminta da kundin zaben da ya kafa hukumar ta CENI da kanta.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

YARJEJENIYAR AIKIN RAJISTAR ZABEN KASAR NIJAR