Hukumar CENI Ta Nijer Ta Fitar Da Sakamakon Zaben 27 Ga Watan Disamba

Zaben Nijer

Alkaluman hukumar CENI na nunin za a fafata a zagaye na 2 a ranar 21 ga watan Fabreru a tsakanin dan takarar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed da Mahaman Ousaman na jam’iyyar RDR ta ‘yan hamayya.

Bayanai sun yi nuni da cewa daga cikin ‘yan takara 30 da suka fafata a zaben shugaban kasa, Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya ne ke kan gaba da kuri’u 1 879 543 yayin da Mahaman Ousman na RDR Canji ke bi masa da kuri’u 811 838, abinda ke nunin za a je zagayen zabe na biyu kasancewar babu wanda ya sami sama da kashi 50 daga cikin 100 na kuri’un da ake bukata don lashe zabe.

Dr Aladoua Amada, shi ne mataimakin shugaban hukumar zabe ta CENI, ya ce alkamun sakamakon zaben da aka sanar daga rumfunan zabe suka fito kuma babu wanda ya samu kason da ake bukata, tun da kundin zabe ya ce dole ne dan takara ya samu kuri'u kashi 51 cikin 100. A saboda haka, ana tsamanin in Allah ya yarda za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Amma duk da haka kotun koli ce za ta tatance sakamakon, a cewar Amada.

Jam’iyyar PNDS Tarayya ta bayyana gamsuwa da wannan sakamako duk kuwa da cewa ba ta cimma gurinta na lashe zabe ba tun a zagayen farko kamar yadda sakataren harakokin zabenta Boubacar Sabo ya bayyana.

Su ma dai ‘yan adawa sun bayyana gamsuwa da wannan sakamako wanda a cewar Ibrahim Maman na jam’iyyar MPN ta kawancen CAP 2021, alama ce da ke nunin ‘yan kasa sun amsa kira.

Ko a bangaren zaben ‘yan majalisar dokokin kasa ma jam’iyyar PNDS mai mulki ke kan gaba da kujeru kimanin 80 daga cikin 166 sai Moden Lumana mai kujeru 19 yayin da MPR jamhuriya ta MNSD NASARA kowacce ta sami kujeru 13, jam’iyyar CPR INGANCI kuma na da kujeru 8 sannan RDR Canji na da kujeru 7.

Yanzu kam hankali ya karkata wajen kotun tsarin mulkin kasa wace ke da hurumin tabbatar da sakamakon wadannan zabubbuka ko kuma ta watsar da shi.

Saurari rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar CENI Ta Nijer Ta Fitar Da Sakamakon Zaben 27 Ga Watan Disamba