Yayinda Najeriya ke kan gaba a tattalin arziki a Afirka kasashen Afirka ta Kudu da Masar suna biye da ita.
Watan jiya rahoton IMF ya ayyana Afirka ta Kudu a matsayin kasar da tattalin arzikinta ya dara na Najeriya kafin a yanzu Najeriya din ta yi mata fintinkau.
Wani masanin tattalin arziki Abubakar Ali ya nuna shakku akan sabon matsayin Najeriya.Yace lissafin IMF na takarda ne kawai. Amma idan an duba cikin kasar menene kasar ke sarafawa? Mutane na fama da rashin aiki da yunwa. Shin mun fi Afirka ta Kudu da Masar sarafa kayan da muke anfani dasu?
Malam Ali yace tattalin arzikin da aka ce ya fi kowace kasa girma a nahiyar Afirka menene ya canza a kasar tun watan jiya? Farashin dalar Amurka yanzu ya haura nera dari hudu. Ta yaya suka samu nasu sakamakon?
To saidai IMF tace girman tattalin arzikin Najeriya a wannan watan ya kai dalar Amurka biliyan 415.8.
Wani masanin tattalin arziki Yushau Aliu yace talakawa ba zasu gani a kasa ba domin tattalin arzikin kasar na hannun wasu mutane kalilan ne. Ya kira ayi gyara domin talakawa su ji a jikinsu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5