Hukumar Bada Agaji, NEMA, Ta Bayyana Dalilin da Yunwa Ta Addabi Yara A Bama

Wata da yaronta da ya kusa mutuwa saboda rashin abinci

Kungiyar nan mai bada agajin aikin likita kyauta,da ake kira da turanci Doctors Without Borders tace a kalla mutane 6 ke mutuwa a kullun sakamakon cutar dake da nasaba da yunwa ko rashin wadataccen abinci a sansanin ‘yan gudun hijirar dake a arewa masu gabashin Najeriya da yakin Boko Haram y araba da muhallansu.

Kungiyar ta kira wannan lamari da ya shafi mutane dubu 24 da aka ajiye a asibiti dake garin Bama a matsayin wani babban balai’in da ya addabi bani adama.

Likitoci dake bada taimako kyauta na duba yaran da yunwa ta yiwa la'ani

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya da ake kira NEMA a takaice tace babban abinda ya haddasa wannan lamari shine fada da akayi cikin ‘yan kwanakin nan tsakanin sojojin kasar da kungiyar Boko Haram.

Mai Magana da yawun hukumar ta NEMA Abdul Ibrahim yace yawancin wadanda basu da cikakken lafiya a sansanin mutane ne da suka iso sansanin daga wasu kebabbun wuraren da suka zame fagen fama tsakanin sojoji da kungiyar ta Boko Haram.

Ibrahim yace wadannan mutanen sun kasance ne a cikin al’ummar da aka kebe su, yadda basu samun abinci, ko magunguna.

Sai dai ko a cikin watan da ya gabata sojojin Najeriya sun bayyana fatattakar kungiyar ta Boko Haram daga tungan su dake Sambisa wanda yake kusa dagarin na Bama.

Kungiyar dai ta Boko Haram, ta kwana biyu tana fada da gwamnatin Najeriya kuma ta samu nasarar kashe mutanen da bazu gaza dubu 20 ba kana ta raba sama da miliyan biyu da matsugunninsu.

Domin a cikin shekarar 2014 da shekarar 2015 kungiyar tayi galaba ga sojojin Najeriya dominko har ta kwace wasu garuruwa, kafin daga baya a kwato su sai dai ko da aka sake kwatosu, sunyi musu lahani.