ABUJA, NIGERIA - Matakin ya biyo bayan bukatar yin hakan don ba wa karin maniyyata damar ajiyar Naira miliyan 4.5 da a ke sa ran farashin kujerar ba zai wuce haka ba.
NAHCON a sanarwa daga mataimakiyar daraktar labaru Fatima Sanda Usara ta dau matakin ne bayan karewar wa'adin farko na karshen watan Disambar da ta gabata, ya zama wasu masu niyyar zuwa ba su kammala tattara kudin ba.
Shugaban hukumar Jala Ahmad Arabi ya saurari kiran da manyan malaman Islama, dattawa da hukumomin alhazan jihohi su ka yi da ke bukatar a kara wa'adin lokacin ajiyar.
Don haka gwamnatin taraiya ta amince da kara wa'adin kuma hakan zai sa gabanin kammalar sabon wa'adin hukumar za ta iya tantance yawan maniyyata da kuma farashin kujerar.
Hajiya Amina Ibrahim dake shugabantar daya daga kamfanonin da su ka samu rejistar jirgin yawo Dija Travels ta bukaci gwamnatin Najeriya ta yi rangwamen Dala ga maniyyata don samun karin matafiya.
Hukumomin Saudiyya sun warewa Najeriya kujeru 95, 000 ga maniyyata inda alamu ke nuna tsadar dala na barazana ga samun adadi mai yawa da za su iya biyan kujerar; don haka kujeru ka iya rara.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5