Sabbin matakan da hukumar alhazan Nigeria ta dauka sun sa hukumomin Saudiyya yadda su bari a soma fataucin kayan abincin Nigeria zuwa Saudiyya lokacin aikin hajji domin jin dadin alhazai.
Hukumar ta alhazan Nigeria ta kuduri aniyar ganin kowane alhaji ya ji dadin rayuwarsa a kasa mai tsarki kwatankwacin kudaden da ya biya kama daga gidajen kwana da motocin shiga da irin abincin da zasu ci.
Shugaban hukumar alhazan Nigeria Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad ya ce tuni aka fara daukan matakan fataucin kayan abincin daga Nigeria. 'Yan kasuwan Nigeria dake da sha'awar kai kayan abinci Saudiyya, yanzu dama ta samu. Za su kai kayan abinci iri-iri hatta shinkafar da aka shuka a kasa.
Sarkin tsafta na Kano kuma shugaban kula da muhalli a tawagar kula da kiwon lafiyar alhazai na kasa, Jafaru Ahmed Gwarzo ya na ganin matakan sun taimaka wajen inganta kiwon lafiyar alhazan dalili ke nan da ba'a samu barkewar wata cuta ba.
Bisa la'akari da yadda tattalin arzikin Nigeria ya ke, Barrister Abdullahi Muhammad ya ce tsarin da suka fito dashi na aika kayan abinci daga Nigeria zuwa Saudiyya hanya ce ta kara kasuwanci tsakanin kasashen biyu tare da habaka tattalin arzikin kasa.
A saurari rahoton Medina Dauda daga Makka
Your browser doesn’t support HTML5