Hukumar Alhazan Najeriya Ta Ce Kudin Bana Bai Gaza Miliyan 1.5

Kaaba

Hukumomin Aikin Hajji na jihohi a Najeriya na ci gaba da bayyana cewa kudin kujerar Hajjin bana bai gaza naira miliyan 1.5.

Hukumar Alhazan Najeriya ta bada izinin sa kudin kujerar hajjin bana, ta yadda jihohi ke bayyana kudin kujerar da bai gaza Naira miliyan 1.5.

Jihar Kaduna da Katsaina na daga cikin wadanda su ka bayyana kudin kujerar, inda a Kaduna bana ba batun karama da babbar kujera wajen guzuri, inda kowa zai samu dala 800.

A Katsina, Hukumar Alhazan jihar ta ayyana kudin kujearar a Naira miliyan 1,519,113,10K .

Daraktan hukumar alhazan jihar Alhaji Muhammadu Abu Rimi, a wata sanarwa, ya bukaci masu niyyar tafiya hajjin su kammala biyan kudin kujerar zuwa karshen watan nan.

Hukumar alhazan NAHCON ta sha nanata dalilin tashin farashin kujerar kan farashin masauki, sufuri, tsadar canjin dala da sauran hidimomi.

A wata zantawa, shugaban hukumar Barista Abdullahi Mukhtar ya ce hatta hidimar da ba a samu yi wa alhazan ba, a kan yi lissafin darajar kudin a dawowa alhazai hakkinsu.

A shekarun baya gwamnatin Najeriya kan yi rangwame kan kudin canjin Naira zuwa dala don a sassauta tsadar kujerar.

Babban sakataren hukumar alhazai na Gombe Usman Gurama ya duba yadda lamarin kan shafi tsadar kujerar "da gwamnati kan ba da tallafi ko rangwame kan canjin Naira zuwa dala. Shigowar wannan gwamnati an dakatar da tallafin da ya sa a ke canzawa alhazai dala kan Naira 305 bisa farashin hukuma, duk da hakan ma sauki ne in an kwatanta da kasuwar canji," in ji shi.

Hakanan Saudiyya kan karbi karin awalaja na RIYAL 2000 ga alhazan da su ka maimaita zuwa hajjin a jere cikin shekarun da ba su gaza biyar ba.

Bincike ya gano cewa wasu daga jihohin kudu maso kudu da kudu maso gabas na da ragin kudin kujerar da ta kan kama miliyan 1.4 da 'yan kai bisa irin hidimar da alhazan jihohin su ka bukaci samu.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Kudin Hajjin Bana Bai Gaza Miliyan 1.5