Babban kamfanin kere-kere na China Huawei ya kaddamar da wata manhajar wayoyin zamani, wacce ya ce ta yiwu ta maye gurbin manhajar Google Android, a kokarin da kamfanin yake yi na kare kansa daga takunkuman Amurka.
Wannan sanarwar da kamfanin Huawei ya yi ta manhajar HarmonyOS, ya nuna irin yadda kamfanin yake ci gaba da bunkasa, wanda shi ne na biyu a duniya wajen kera wayoyi na zamani kuma babba wajen kerawa kamfanonin waya cibiyar sadarwa, da ya kirkiro da fasaharsa da za ta taimaka masa wajen dogaro da kamfanoni Amurka.
A watan Mayun da ya gabata, Amurka ta dakatar da barazanar da take na sayar da wayoyin zamani na Huawei na rage yadda suke amfanin da manhajar Android da kuma toshe wani bangaren kamfanin Google na harrufa da ya shafi wakoki da kuma wasu sauran abubuwan da suke cikin manhajar.
Shugaban da yake kula da bangaren da ake siyar da kayayyakin kamfanin Huawei, Richard Yu, ya fada a wajen wani taron masu kirkirar fasahohin zamani a garin Dongguan na Lardin Guangdong da ke China cewa, suna so su ci gaba da amfani da manhajar ta Android.
“Duk da haka, idan ba za mu iya ci gaba da amfani da ita ba anan gaba, to za mu sauya da sauri zuwa manhajar HarmonyOS.” A cewar Yu.