Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya Honarabul Yakubu Dogara, ya ce ‘yan sandan ba su bi ka’ida ba kan yadda suke neman Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi, dan majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar cikin garin Bauchi, a saboda haka za su kalubalanci hukuncin a kotu.
A wani taron manema labarai da Mr. Yakubu Dogara ya kira, ya zargi hukumar ‘yan sanda da keta hakkin dan majalisar, domin ya ce akwai ka’idoji da ake bi idan ana neman dan majalisa ya gabatar da kansa gaban hukumar ‘yan sanda.
Iyalan Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi, da hukumar ‘yan sanda ke nema, sun bayyana cewa lamarin ya basu mamaki ya kuma tada musu hankali sosai.
A nata bangaren hukumar ‘yan sanda a ta bakin kwamishinanta Aminu Alhassan, yace ana neman dan majalisar ne a matsayinsa na Yakubu Shehu Abdullahi kuma an bi dukkan ka’idoji da dokar kasa ta Shimfida.
'yan sanda na zargin dan majalisar ne bayan da ta fara bincike kan wani rikici da ya barke a garin Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu 15.