Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi tir da takaddamar da ta kunno kai kan hana wata daliba da ta saka hijabi shiga zauren rantsar da daliban lauyoyi inda aka ba su takardar shaidar kama aiki.
A makon da ya gabata ne aka hana Amasa Firdaus shiga wajen bikin a jam’iar Ilori da ke jihar Kwara, saboda ta sanya hijabi hade da kanayn aikin lauya.
Amma Sultan Abubakar ya ce, hijabi sutura ce da ke nuna kamala wanda addinin Musulunci ya umurci ‘ya’ya mata su saka, kamar yadda jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito.
A yau Asabar Sarki Abubakar, ya bayyana hakan a wani taron jama’ar Musulmi da aka yi a Legas a karo na biyar.
Sultan wanda shi ne shugaban Majalisar Koli ta Musulman Najeriya, ya kuma nuna takaici da fargabarsa kan yadda wannan lamari zai rika barazana ga ‘ya’ya mata masu saka hijabai, kamar yadda jaridar ta wallafa.
Masu ruwa da tsaki a wajen taron rantsar da daliban, sun hana Firdaus shiga zauren ne saboda a cewarsu shigar da ta yi da hijabi ya saba ka'ida.