Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Kalubalanci 'Yan Jarida

Ministan Tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi kira ga ‘yan jaridar kasar da su rika bai wa hukumomin tsaro hadin kai yayin da suke gudanar da ayyukansu.

A cewar Darektan yada labarai a hedkwatar tsaron kasar, Brigadier General John Agim, yayata labaran da ke fitowa daga bangaren mayakan Boko Haram tamkar taimakawa ayyukan ta’addanci ne.

“Duk dan jaridar da ke rawar jiki wajen aika rahoto kan abin da Boko Haram ta yi ko ta ce, ko kana so ko ba ka so, ya zama kana masu aiki kenan.” In ji Agim.

Ya kara da cewa, hedkwatar tsaron ta Najeriya na matukar bukatar hadin kan kowa da kowa wajen yaki da masu ta da kayar baya a rewa maso gabashin Najeriya.

“Saboda wannan yaki ne mai wuyar sha’ani, muna yakar wadanda sun san mu amma mu ba mu san su ba.” In ji Agim.

Wadannan kalamai na hedkwatar tsaron na zuwa ne kwanaki kadan bayan da sojojin Najeriya suka kai wani samame a ofishin gidan jaridar Daily Trust da ke Abuja, bayan wani labari da kamfanin ya wallafa.

Sojojin sun zargi gidan jaridar da wallafa wasu bayanai da suka jefa harkar tsaron kasar cikin hadari.

Ko da yake, samamen da aka kai wa jaridar ta Daily Trust ya janyo aka yi ta sukar jami’an tsaron a ciki da wajen Najeriya, amma masana a fannin tsaro sun ce akwai bukatar ‘yan jarida su rika takatsatsan wajen wallafa bayanan tsaro.

“Irin wadanan labarai a duk lokacin da aka yi su, ya kamata a rika tace su a tabbatar da cewa ba su yi karo da abubuwa na tsaro ba.” In ji Air Commander Ahmed Tijjani Babagamawa mai ritaya, wanda kan yi sharhi kan tsaro.

Tun daga shekarar 2009, Najeriya ke fama da hare-haren ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, musamman a arewa maso gabashin kasar

Ayyukan kungiyar ya salwantar da dubban rayukan jama’a a kasar ta Najeriya da makwabtanta.

A shekarar 2015 an samu lafawar rikicin, amma a baya-baya nan, mayakan kungiyar ta boko Haram, sun kara zafafa hare-haren da suke kai wa.

Wasu bayanai sun yi nuni da cewa yanzu haka wasu garuruwa akalla shida ciki har da garin Baga a yankin jihar Borno sun sake fadawa hannun mayakan, amma dakarun na Najeriya sun musanta wannan ikrari.

Saurari rahoton da Hassan Maina Kaina ya hada kan wannan batu:

Your browser doesn’t support HTML5

Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Kalubalanci 'Yan jarida - 2'29"