Hawa Da Saukar Tattalin Arzikin Najeriya

Karancin man fetur a Najeriya, Mayu 26, 2015

Tattalin arzikin Najeriya ya sha fama da fadi tashi daga shekarun 1960 zuwa 1970 a kowanne shekara, tattalin arzikin wanda ya habaka da kashi uku da digo daya 3.1 wanda kuma masana ke ganin yayi.

A Najeriyar daga shekarun 1970 zuwa 1978, tattalin arzikin ya kara hawa sama sosai da kashi shida da digo biyu 6.2 na kowacce shekara, a kusan karshen wannan lokaci shugaban kasa na wancan zamani Janar Murtala Muhammad ne ya bullo da wasu tsauraren matakai na karfafa tattalin arzikin, ta hanyar sallamar duk jami’an gwamnatin dake da alaka da rashawa.

Haka zalika gwamnatin soja ta Obasanjo da ta farar hula ta Shehu Shagari duk sun fito da shirin “A Koma Gona” domin karfafa tattalin arzikin, biyo bayan abinda masu sharshi ke cewa matsalolin da suka yiwa kasar katutu.

Soji sun kifar da gwamnatin Shagari, inda shugaba Buhari ya karbi mulkin, ya kuma bullo da shirin “Yaki Da Rashin Da’a Da Cin Hanci Da Rashawa” duk dai don a inganta tattalin arziki.

Itama gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta bullo da shirin “Kowa Yaji A Jikin Sa” shirin da mafi yawan ‘yan Najeriya ke ta kuka da shi a wancan lokaci, tattalin arzikin dai ya ci gaba da habaka kama daga lokacin da aka sami ‘yancin kai akalla da kashi hudu, amma biyo bayan samun man fetur a kasar wanda ya shafi rawar da aikin gona ke takawa a sha’anin tattalin arzikin kasa.

Man fetur shine babban abinda Najeriya ta dogara a yanzu, baya ga kuma ga hukumar kwastam da hukumar tara kudaden shiga ta kasa, a jawabin shugaba Buhari na jiya albarkacin samin ‘yancin kan Najeriya yace, “ana daukar sabbin matakai don tsaftace kamfanin mai na kasa wato NNPC, a kuma inganta aikace aikacensa don a kawar da cin hancin da sukayiwa kamfanin tarnaki, zakuma a gyaggyara dukkannin matatun man fetur na Najeriya, da hakan zai basu damar yin aiki baji ba gani. A kuma dakatar da fitar da gurbataccen man mu ana kuma shigo mana da tatatce cikin wani yanayi na cuwa cuwa.”

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa baya ga kamfanin NNPC, kazalika za’a kuma a binciki sauran hukumomin da ke tara kudin shiga a kasar, irin su babban Bankin Najeriya da Hukumar Kwastam da hukumar tara kudin shiga ta kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hawa DA Saukar Tattalin Arzikin Najeriya - 2'25"