Sakamakon karuwar bukata saboda bukukuwan karshen shekara, hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Najeriya ta karu zuwa kaso 34.80 cikin 100 daga kaso 34.60 da yake a watan Nuwamban daya gabace shi, kamar yadda hukumar kididdigar Najeriya (NBS) ta bayyana a yau laraba.
Hukumar kididdigar ta bayyana hakan ne a rahoton sauyin farashin kayan masarufi na baya-bayan nan wanda ke auna sauyin da aka samu akan kayayyakin bukatun rayuwa.
Hauhawar farashin kayayyakin masarufin na watan Disemban 2024 ya nuna cewa an samu dan sauyin kaso 0.20 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Nuwamban da ya gabace shi.
“Hakan ta faru ne sakamakon karuwar bukatar kayan masarufi na lokacin bukukuwan watan Disamba,” a cewar rahoton.
A wani labarin kuma, hauhawar farashin kayan abinci a watan Disamban 2024 ta kai kaso 39.84 cikin 100 a bisa kididdigar daga shekara zuwa wata, inda ta karu da kaso 5.91 cikin 100 idan aka kwatan da yadda take a watan Disemban 2023 (33.93%)