KUMASI, GHANA - Wannan sabon adadin ya zarta wanda aka gani a watan Mayun bana wanda ya kai kashi 27.6 bisa dari. Sai dai akaron farko tun shaikarar 2004 da hauhawan farashin kayayyaki ya kai kashi ashirin da tara sai kuma bana awatan Yuni da aka samu fiyeda hakan.
Masana tattalin arziki na danganta hauhawar farashi kayayyaki da tsadar rayuwa bisa tashin kudin motar haya.
Mallam Abu Naeem Afandi masanin tattalin arzki a Ghana ya ce wannan matsala akwai damuwa sosai kuma tashin kudin motar haya ne dalilin hauhawan farshin kaya a wanan karon.
A nasa jawabi mataimakin shugaban kasar Ghana Dakta Mahmud Bawumia ya bayyana cewa gwamnati na daukan matakan da suka dace domin ganin an shawo kan wannan iftilai, amma a wannan karo Ghana zata samarda kamfanonin cikin gida domin dagaro da kai.
Sai dai kuma burin da gwamnatin jamiyyan NPP take kokarin cimma shine kaucewa dukufa akan kasashen ketare domin neman tallafi, wato Ghana Beyond Aid, amma kuwa abaya bayanan a kasar na nuna cewa ta tuntubi IMF, biyo bayan yakin Ukraine da Rasha da cutar coronavirus, sun bada gudunmuwa gurin tabarbarewar tattalin arzkin kasar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5