Hattara Dai Masu Amfani Da Wayoyin Hannu

FILE - with the new app on their mobile device, people can receive and share information in real-time in the event of a health crisis, epidemic(s), and natural disasters.

Wayar Salula da sauran kayyayakin fasaha na wannan zamani sun taimakawa ci gaban al’umma da duniya baki ‘daya, idan aka duba yadda aikawa da karbar sakonni ya zamanto abu mai sauki idan aka kwatanta shi da zamanin baya.

A daya bangare kuwa kayayyakin fasaha sun shiga zukatan mutane ta yadda wani lokacin kan kai wasu mutane ga hallaka ba tare da saninsu ba. wani nazari da aka gudanar na nunin mutane Biliyan 6.8 ne suka mallaki wayoyin hannu cikin yawan mutanen duniya Biliyan 7, idan aka duba duk mutane 96 cikin 100 suna da wayar hannu.

Duk inda aka duba kan hanya a duk biranen dake duniyar nan za’a ga mutane na amfani da waya ko suna magana, ko suna aika sakon karta kwana, harma sauraren wakoki da yin wasanni. Babban abinda dubawa anan shine mutane basa mayar da hankali kan abinda suke yi musammam idan suna tafiya akan titi ko suna tuka ababen hawa.

A karshen makon da ya gabata ne aka fitar da labarin wani ba Amurke da ya fada wani rami har yayi asarar ransa, mutanen da suka ganewa idansu faruwar hakan sunce matashin mai shekaru 33 da haihuwa ya afka ramin sakamakon mayar da hankalin sa ga amfani da wayar hannu. Labarai daga sassan duniya daban daban suna nunin yadda ake samin karuwar hatsari duk a dalilan wayoyin hannu.

To jama’a sai ayi hattara domin masu iya magana na cewa Lafiya Jari ce.