Hatsarin Kwale-Kwalen Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 24

  • VOA Hausa

Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

A yau Alhamis, masu ninkaya suka tsamo karin gawawwaki 8 daga cikin kogin da wani kwale-kwalen da mahalarta taron Maulidi ya kife a garin Gbajibo, na karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.

Aikin tsamo gano gawawwakin ya kawo adadin mutanen da suka mutu zuwa 24, a cewar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wani kwale-kwale daya taso daga garin mundi ya kife, ‘yar tazara daga inda yake nufin zuwa.

Babban daraktan, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Alhaji Abdullahi Baba-Arah, yace an riga an birne 16 daga cikin gawawwakin mutanen da aka tsamo a jiya Laraba a garin Gbajibo.

Arah ya kara da cewar ana cigaba da aikin nema da ceton wadanda hatsarin ya rutsa dasu a bisa hadin gwiwar jami’an nsema da masu ninkayar yankin.