Hukumar bada agajin gaggawa ta Neja (NSEMA) ta bayyana cewar an samu nasarar ceto fiye da mutane 150 daga hatsarin kwale-kwalen daya afku a garin Gbajibo dake Karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Ya kara da cewar har yanzu ba’a kai ga tantance musabbabin kifewar kwale-kwalen ba, inda yace a halin yanzu suna kara tsananta aikin nema da ceton wadanda al’amarin ya rutsa dasu.
“Hatsarin kwale-kwalen ya faru ne a daren jiya 1 ga watan Oktoba, da misalin karfe 8 da rabi na dare a daidai mahadar kogin neja da madatsar ruwa ta jabba.
“Kwale-kwalen na dauke ne da kusan fasinjoji 300, galibinsu mata da kananan yara, kuma yana kan hanyarsa ne daga garin mundi zuwa gbajibo domin halartar bikin maulidi.
“Hukumarmu na yin hadin gwiwa da ma’aikatar sufuri ta jihar da kwamitin bada agajin gaggawa na karamar hukumar mokwa, da masu ninkaya da ‘yan sa kan cikin al’umma domin gudanarwa tare da sa ido akan aikin nema da ceton wadanda hatsarin ya rutsa dasu,” a cewarsa.
Baba-Arah ya kuma bada tabbacin cewar, “NSEMA za ta samar da sahihan bayanai game da lamarin cikin lokaci.”
Dandalin Mu Tattauna