Haruna Wakili Ya Ce Lallai An Yiwa Matasa Fashi Da Makami A Siyasa

Haruna Wakili shugaban kungiyar kare hakkokin matasa a gwamnatance, wadanda ake dannewa hakki, wato Youth Liberation Front, ya ce gwamnatin jihar Kano zata sami tirjiya tsakaninta da matasa domin kuwa an tauyewa matasa damar da ta dace wajen zabar abinda suke so.

Sakataren kungiyar Haruna Wakili ne ya bayyana haka a yayin wata hira da Muryar Amurka Baraka Bashir a birnin Kano.

Ya ce zaben da ya gabata a jihar Kano lallai an yi wa matasa fashi da makami a fannin siyasa, domin a cewar sa ko a zabukan farko na shugaban kasa matasa sun zabi Buhari ne a sanadiyar rashin babu yadda zasu yi.

Ya kuma ce lallai a 'yan takarkarun biyu da suka tsaya a takarar mulkin shugaban kasa dukkaninsu babu wanda ya cancanta, a rashin babu ne suka zabi shugaba Buhari. Ya kara da cewa a bisa al’ada akwai wasu kudade da gwamnati ke fitarwa na agent agent a lokutan zaben, amma a wannan karon shugaba Buhari ya hana fitar da wadannan kudaden bayan an ja matasa a jiki, an kuma basu damar su fito takarar domin kawo sauyi, sai da aka zo daf da zaben sannan suka san ba’a za’a fitar da kudin ba, abinda ya jefa matasan cikin halin ha’ula’I da fargaba, har suka rasa madafa.

Kwamared Wakili ya ce an yi wa matasa shigo-shigo ba zurfi a wannan zaben da ya gabata.

Da aka zo wannan zabe na gwamna, sakamakon matasa basu gamsu da abinda gwamnatinsa ta ke yi ba, ya sa suka yi kokarin kawo sauyin gwamnati ta yadda za’a dama da su domin kawo sauye-sauyen da suke bukata musamman ganin yadda da dama matasa suna fama da matsalolin rashin ayyukan yi.

Your browser doesn’t support HTML5

Haruna Wakili Yace Lallai Anyi Wa Matasa Fashi Da Makami Na Siyasa 07'03