A shirinmu na nishadi a yau DandalinVOA bakunsi mawaki Sani B Haruna yayi, mawakin nanaye wato soyayya, wanda ya ce soyayya ita ce silar zaman duniya, inda ya ke cewa a duk yanayi na rayuwa sai da soyayya ne ake samun zaman lafiya.
Ya ce idan aka ce soyayya ba lallai sai tsakanin saurayi da budurwa ba, akwai soyayya tsakanin aboki da aboki, ko tsakanin wannan al’umma da wancan sai da soyayya ne suke zaman lafiya.
Sani ya ce ya shafe shekaru bakwai kenan yana sana’a ta waka, kuma kamar sauran mawaka ya ce bai fuskanci wata matsala ba domin kuwa akwai kyauwawar fahimta tsakaninsa da iyayensa.
Mawakin ya ce duk da cewa babu abinda baya faruwa da zarar mutun yana wata sana'a ta sa, sai dai shi matsalar da ya fuskanta, kalubalen da ya fusanta bai wuce kyashi da rashin bada hadin kai da wasu manyan mawaka kan nunawa, ga masu tasowa mussman ma a lokutan da suke kokarin tashi.
Baya ga nan ya ce ya fuskanci matsaloli a Studio a lokacin da yake yunkuri yin recording na wakokinsa, mawakin ya ce banda wannan yakan yi wakar da ta shafe zaman lafiya jefi-jefi, mussaman ma a lokutan da kasar Najeriya ta fara fuskantar matsaloli na tsaro tsakanin al’umomi.
Your browser doesn’t support HTML5