Harkokin Tsaro Sun Yi Wa Al'adar Tashe Cikas A Wasu Sassa

A yau DadalinVOA yayi duba ne kan al'adar nan ta tashe, wacce ake farawa da zarar an shigo goma ta tsakiya ta azumin watan ramadana bayan Nalako ya daga tuta.

Yara da manya har da mata ne ke gudanar da tashe a mafi yawan lokuta da rana ko da daddaresuna shiga gida-gida ko shago shago da ma lunguna domin samun hatsi ko kudi a gidajen da sukai tashen.

Auwalu Kabiru Yakasai, daya daga cikin wadanda DandalinVOA ya samu a kasuwar rimi lokacin da suke gudanar da tashe ya ce suna gudanar da tashen ne domin nishadantar da masu azumi tare da tara kudade wasu lokuta ma har da kayan gwari ko hatsi.

Shima wani da muka same shi a shagonsa kuma yara suna masa tashe malam Auwalu Uba Yaksai, ya ce suna farin ciki da tashe amma matsalolin tsaro sun haddasa cikas ga harkar.

Ya kara da cewa matsalar tsaro ta sa a yanzu ma ba'a ganin Nalako na yawo a gari domin gudanar da tashe kamar yadda aka saba yi a al'adar malam bahaushe.

Your browser doesn’t support HTML5

Harkokin Tsaro Sun Yi Wa Al'adar Tashe Cikas A Wasu Sassa