LEGAS, NAJERIYA - A lokacin wannan yaji da maaikatan sun rufe kofar shiga jami'ar tare da hana masu zurga zurga sukunin gudanar da harkokin su na yau da kullum.
Tun daga kofar shiga jami'ar zakaga ma'aikata dauke da kwalaye da aka rubuta" gwamtanin tarayya ki biya mu albashin mu" da kuma wani mai cewa " Gbajabiamila kaci amanar mu, bamu yarda ba".
Kwamred Abiodun Olayinka shine shugaban Kungiyar na jami'ar legas wanda yake cewa- mun fara yajin aiki na kwanaki 7 domin neman a biya mu hakkokin mu,kuma munbi dukkanin hanyoyin lalum amma babu biyan bukata,yajin aiki ne kawai yaren da gwamnati keji"
Suma dai daliban sun sheda mani cewar yajin aikin yq shafe su ta fannobi da dama kamar yarda wani dalibi mai suna Adekunle Abdulateef yace" muna jarabawa don haka yajin aikin ya shafi wasu fannoni ne,kqmqr dakin kqratu da ofisoshin malamai da ma'aikatan tsaro da dakunan ba haya duk wayannan gurqre ne da masu yajin aikin ke aiki, yakamata a daidai domin komai ya dawo dai dai".
Bayan yajin aikin malamai da ma'aikatan jami'oi na shekara tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da albashin malaman.
Daga bisani ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci a biya albashin, amma kuma ba tare da biyan ma'aikatan da ba malamai ba albashin su na wata hutu, abunda kuma ya sanya su shiga yajin aiki.