Harkoki sun fara komawa kamar da a Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso bayan harbe-harben tsakar dare a fadar shugaban kasa

Shugaba Blaise Compaore na kasar Burkina Faso.

Manyan titunan birnin Ouagadougou sun fara cika da jama’a bayan harbe-harben bindigogin da aka rika ji a daren jiya Alhamis a fadar shugaban kasar Burkina Faso, abin ya baiwa jama’a tsoro kwarai da harbe-harben suka fara watsuwa zuwa wasu sassan babban birnin.

Kafofin labarai, Juma’a a babban birnin kasar Burkina Faso sun bada rahotannin cewa kamar almara aka rika jin harbe-harben bindigogi da hakan ya janyo tashin hankali harda kokkona gidaje da satar kayan jama’a. Ashe zanga-zangar rashin amincewa kin biyan kudaden hayar gidajen dogarawan fadar shugaban kasa ne ya janyo harbe-harben.Shaidun gani da ido suka ce an fara jin harbe-harben daga barikokin manyan hafsoshin soja, sannan harbe-harben suka watsu zuwa sassan birnin Ouagadougou. Bbau wani rahoton rasa ran da aka samu.

Amma lokacin da ake wadannan harbe-harben shugaba Blaise Compaore baya fadar shugabankasa, ba’a kuma san inda ya shige ba. Sai dai daman an shirya shugaban kasa zai yi wata tattaunawa ta musamman yau Juma’a, tare da jagoran jami’an shiga tsakani a rikicin Ivory Coast da MDD ta tura.