Harin Sari Ka Noke da Boko Haram Keyi Ba Abun Mamaki Ba Ne

Janar Buratai da sojojinsa

Kakakin hedkwatar rundunar tsaron Najeriya Bigediya Janar Rabe Abubakar yace sabbin hare-haren sari ka noke da mayakan Boko Haram keyi ba abun mamaki ba ne kuma alama ce ta tsoro saboda an dauki matakan gamawa dasu.

A cewar masana harkokin tsaro kamar su Air Commodore Baba Gamawa yakin sari ka noke da ake gani kwanan nan ba sabon abu ba ne.

Yace tunda aka fatattakesu daga inda suka yi kakagida abun da zasu yi shi ne su bazu suna kwantan bauna wa duk dakarun sojin Najeriya domin su dinga kai hari jefi-jefi.

Abun da yakamata sojoji suyi yanzu shi ne suyi hattara saboda 'yan Boko Haram sun bazu, sun shiga sako-sako sun boye. A duk lokacin da suka ji motsin sojojin Najeriya zasu fito da karfi su afka masu. Ya kira a yi bincike a san duk inda suke domin a hanasu sake fadawa mutane.

Aliko Harun jami'in leken asirin sojojin Najeriya yace duk 'yan Boko Haram da aka kora daga Sambisa suna dajin Gasa.

Rundunar sojojin Najeriya ta sha alwashin bin sawun 'yan Boko Haram din a duk inda suka shiga da zummar gamawa dasu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Sari Ka Noke da Boko Haram Keyi Ba Abun Mamaki Ba Ne - 2' 51"