Harin Najeriya: Sama Da Dalibai 300 Ne Har Yanzu Ba A Gano Su Ba

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Najeriya: Sama da dalibai 300 ne har yanzu ba a gano su ba

Wadanda suka yi garkuwa da dalibai sama da 300 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake Kankara, a jihar Katsina a Najeriya sun bukaci gwamnati ta biya su kudin fansa domin sako yaran.

Wadanda suka yi garkuwa da dalibai sama da 300 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake Kankara, a jihar Katsina a Najeriya sun bukaci gwamnati ta biya su kudin fansa domin sako yaran.

Fiye da dalibai 300 ne ba a gani ba tun bayan harin da aka kai makarantar ta maza a daren Juma’a, in ji gwamnan Katsina Aminu Masari.

A ranar Asabar ne sojoji da ‘yan sanda suka fara aikin kubutar da daliban, a cewar gwamnati.

Sojojin sun yi artabu da 'yan bindigar bayan an gano maboyarsu a dajin Zango / Paula a ranar Asabar, a cewar wata sanarwa ta shugaba Muhammadu Buhari.

A lokacin da aka kai wa makarantar hari, ‘yan sanda sun yi bata kashi da‘ yan bindigar, lamarin da ya bai wa dalibai da dama damar tsallake katangar makarantar don guduwa, a cewar mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Katsina, Gambo Isah.

Makarantar ta na da ɗalibai sama da 600.

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Muhammadu Buhari, da jihar Katsina.