Jami'an Afghanistan sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai a yau Juma'a yayi sanadiyyar mutuwar a kalla 'yan sanda shida da kuma raunana mutane 10 ciki har da Kwamandan yanki a lardin Kandahar da ke kudancin kasar.
Dan kunar bakin waken ya kutsa ne cikin wani chaji ofis da ke gundumar Maiwand da wata mota irin ta soja da ake kira Humvee, wadda aka makare ta da nakiya.
Kwamandan 'yan sanda na shiyyar mai suna Sultan Muhammad ya shaidawa muryar Amurka cewa, tashin bam din yayi sanadiyyar tarwatsa ofishin 'yan sandan da kuma gidanjen mutanen da ke makwabtaka da su.
Ya kara da cewa ‘yan sandan da aka girke a mashigar farko, sun yi kokarin tsayar da motar da ta yo dakon bama-baman da nauyinsu ya kai kimanin kilo dubu uku ta hanyar budewa motar wuta, amman direban ya samu nasarar kaiwa ga kofa ta biyu kafin ya tayar da nakiyoyin.
Tuni dai ‘yan Taliban suka dauki alhakin kai wannan hari.