Harin Da Isra'ila Ta Kai A Gaza Ya Hallaka Falasdinawa 3

Wani bafilasdine da ya rasa ransa a zanga-zanga kan iyakar Gaza da Isra'ila.

Ma'aikatar kiwon lafiya a Gaza, ta ce an kashe Falasdinawa 3 a jiya Laraba lokacin da Isra'ila ta kai hari gabashin birnin Gaza.

Sojojin Israila sun ce sun auna "sansanin mayakan Hamas ne a zirin Gaza" bayan da aka kai wa rundunar sojojin Isra'ila da ke bakin iyaka hari, har aka raunata soja daya.


Wannan fadan na baya-bayan nan ya zo ne da kwanaki kadan bayan da shugabannin kungiyar ta Hamas da Isra'ila suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, da zummar sassauta rikicin.


Sai dai wannan yarjejeniyar ta rushe a karshen makon da ya gabata bayan da wani Bafalasdine ya bindige wani sojan Isra'ila.


Wannan ne yasa Isra'ila ta mayar da martini da wani gagarumin hari wanda ya janyo fargabar barkewar wani yaki tsakanin Isra'ila da Hamas, wanda daman sun gwabza yaki har sau uku tun a shekarar 2008.