Harin da Aka Kai Kan Turkiya Ya Hallaka Mutane 36 Tare da Jikata Wasu 147

Gawarwaki a kasa cikin harabar tashar jiragen saman Istanbul, babban birnin Turkiya

Da safiyar yau ne Prime Ministan kasar Turkiyya Binali Yildirin yayi kira da hada kai, a dai-dai lokacin da mutanen da suka mutu a harin bomb da aka kai tashar jirgin saman kasar ke karuwa zuwa 36.

Daya daga cikin ‘yan maailisar zartaswan gwamnatin kasar yace cikin adadin da suka mutun harda su ‘yan kunar bakin waken su 3 wadanda suka iso tashar jirgin cikin tasi da yammacin jiya Talata, inda da farko suka shiga budewa mutanen dake zirga-zirga a wannan tashar wuta a harbin mai kan uwa da wabi, kafin daga bisani suka tada bomb musammam da suka ga ‘yan sanda sun kusa kai garesu.

Babban jami'in yace mutane da yawa sunji rauni. Da farko mahukunta sunce wadanda suka ji rauni sun kai 60 amma daga bisani adadin ya haura har zuwa 147.

Wakilin Muryar Amurka dake Istanbul Dorian Jones yace daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya tada nasa bomb din ne a wajen tashar jirgin inda mutane ke sauka daga jirgi.

Kuma wannan wurin sau tari zaka taras dashi cike da dan mutum suna jiran abin hawa, kana sauran biyu ko anyi imanin cewa sunyi kokarin shiga cikin tashar wanda yake cike da ‘yan sanda amma basu samu nasarar hakan ba.

Sai dai kawo yanzu ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin, wanda yazo dai-dai da lokacin da gwamnatin kasar take fama da tagwayen barazanar masu tsananin kishin addini dake kudu maso gabashin kasar.

Sai dai da yammacin jiya Talata wani jamiin leken asiri na kasar Faransa ya shaidawa Muryar Amurka cewa wannan aikin ta'addancin yafi kusa da ‘yan kungiyar ISIS fiye da kurdawa dake kasar.Sai dai kuma bai kara wani bayani ba baya ga wannan.

Masu aikin agaji suna kwashe wadanda suka jikata