Harin da Aka Kai Gambia Ta'adanci ne

Shugaban Gambia Yahya Jammeh

Shugaban kasar Gambia yace sojojinsa basu da hannu a harin da aka kai a kasar makon jiya

Sojojin dake goyon bayan shugaban Gambia suna bi gida-gida a Birnin Banjul domin zakulo wadanda ake zaton su ne suka kai hari akan fadar shugaban makon jiya.

Shugaba Yahya Jammeh ya fada jiya Alhamis cewa ta’adancin safiyar Talatar da ta gabata ba yunkurin juyin mulki ba ne domin sojojin kasar suna goyo bayansa.

Mr. Jammeh yace hari ne na ‘yan ta’ada dake samun goyon bayan wasu da suke kasar ketare.

Shugaban yace babu daya daga cikin sojojin kasar da yake da hannu a ta’adancin amma su ne ma suka dakile yunkurin. Sabili da haka ba za’a ce sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatinsa ba kamar yadda ya karanta a wasu kafofin labaru. Harin na wasu ‘yan ta’ada ne kuma an san inda suka kafa sansaninsu.

Shi dai shugaban baya cikin kasar yayin da lamarin ya faru.