Harin Boko Haram Ya Hallaka Sojojin Chadi 40

  • VOA Hausa

Shugaban Rukon Kwaya Na Chadi Mahamat Idriss Deby

Sanarwar da fadar shugaban kasar Chadin ta fitar tace an kai harin ne kusa da garin Ngouboua dake shiyar yammacin kasar, “inda ya hallaka kimanin mutane 40.”

Harin da kungiyar Boko Haram mai ikirarin jihadi ta kai cikin dare ya hallaka kimanin sojojin Chadi 40 a kusa da kan iyakar Najeriya, abinda ya sabbaba wani samamen soji domin farauto ‘yan bindigar, a cewar gwamnati da wasu majiyoyi a kasar a yau Litinin.

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan wata tungar tsaro mai dauke da sojojin Chadi 200 da yammacin jiya Lahadi a yankin tafkin Chadi, yankin dake zama mafaka ga kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban, kamar yadda majiyoyin yankin suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Chadin ta fitar tace an kai harin ne kusa da garin Ngouboua dake shiyar yammacin kasar, “inda ya hallaka kimanin mutane 40.”

Sanarwar ta kara da cewar, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya ziyarci wurin da al’amarin ya afku da safiyar yau Litinin sannan ya kaddamar da wani samame “na bin sawun maharan har maboyarsu duk nisanta tare da farauto su.”

Kwamandan tungar tsaron na cikin wadanda harin ya hallaka, a cewar wani babban hafsan sojan da ya nemi a sakaya sunansa.

Babban hafsan ya kara da cewa, maharan sun samu damar kwace harsashai da kayan aiki kafin su janye.

A cewar majiyar da ta nemi a sakaya sunanta, mayakan Boko Haram din sun kwace tungar tare da wawushe albarusai da kone motocin dake dauke da manyan bindigogi.”

“eh, muna da wadanda harin ya rutsa dasu da dama, amma an shawo kan lamarin kuma dakarunmu na kokarin farauto abokan gabar,” kamar yadda gwamnan yankin, Janar Saleh Haggar Tidjani, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.