Harin Ban A Mosul Ya Nuna Cewa Akwai Sauran Rina A Kaba

Harin da aka kai da wani bam da aka ajiye a cikin wata mota a garin Mosul na kasar Iraq, ya karfafa fargaban da wasu masu nazari suke da ita, na cewa taron dangin da kasashen duniya suka yi wa kungiyar ISIS ya raunana karfin mayakanta.

Amma kuma ya kasa baiwa kasashen dake yaki da ita nasara ta fannin siyasa, duk da cewa yau kwannaki 190 tun lokacin da sojojin kasashen duniya, a karkashin jagorancin Amurka, suka soma faman fitarda mayakan ISIS daga garin na Mosul, amma har yanzu abin ya gagara, tunda har yanzu akwai tarin mayakan ‘yan tawayen a sassa daban-daban na birnin.

Ko a cikin watan jiya ma IS ta tada wani bam na mota a gundumar Zuhur, dake gabashin Mosul, inda mutane hudu suka rasa rayukkansu, wasu 14 suka jikkata.

Tun cikin watan Janairun da ya gabata ya kamata ace an raba Zuhur da ‘yantawayen IS amma wannan harin da suka kai na baya-bayan nan ya nuna cewa har yanzu suna nan daram zaune a wurin.