Harin Amurka A Somalia Ranar Asabar Ya Hallaka Mayakan al-Shabab 27

Kungiyar al-Shabab

Wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai Somalia ranar Asabar ya yi sanadiyar mutuwar mayakan al-Shabab 27 kamar yadda runudunar sojojin Amurka dake nahiyar Afirka suka sanar

Wani harin sama da jiragen yakin Amurka suka kai a ranar Asabar a Somalia, ya hallaka mayakan Al Shabab 27, a cewar, rundunar dakarun Amurka mai kula da shiyyar Afirka.

Rundunar ta bayyana hakan ne a sakon Twitter, tana mai cewa harin an kai shi ne tare da hadin gwiwar gwamnatin Somalia a yankin Bosaso da ke yankin Puntaland mai kwarkwaryan ‘yancin kai.

A cewar rundunar ta Amurka, ba a kashe farar hula ko daya a harin ba.

Hare-haren Amurkan a cewarta, na kaikaitar sansanonin da ake horarwa da mayakan kungiyar da kuma maboyarsu a baki dayan kasar ta Somalia da kuma yankin.

A dai ranar Alhamis din da ta gabata, wani harin saman da Amurkan ta kai akan mayakan na Al Shabab, ya hallaka mutum 12 a can kudancin Mogadishu.

Harin na ranar Asabar na zuwa ne, bayan da mayakan na Al Shabab suka kai hari a wani sansanin soji a Puntland, inda suka yi ikararin kashe sojoji biyar, kana suka ce sun jikkata wasu bakwai tare da lalata kayayyakin sojin kasar ta Somalia.