Hari a New York: Mutane Biyar Na Nan Rai Kwakwai, Mutu Kwakwai

  • Ibrahim Garba

Birnin New York

Gwamnar New York, Kathy Hochul, ta ce mutumin nan da ya bude wuta cikin jirgin kasa a Yankin Brooklyn yayin da ake harmar tafiye tafiye da safe, ya na da hadarin gaske, kuma har yanzu ba a kama shi be.

“Mu na kira ga jama’a cewa kowa ya kula sosai,” a cewar Hochul ga manema labarai a wurin da ake kan bincike. Ta kara da cewa, “Wannan yanayi ne na harbe harben da ba a ga karshensu ba.”

Ita kuwa Kwamishinar ‘Yan sanda, Keechant Sewell, cewa ta yi, “A halin yanzu babu wani abin fashewa a jirgin.” Rahotannin farko sun nuna cewa da alamar akwai wasu abubuwan fashewa.

Duk da ya ke ba a san dalilin maharin ba, Kwamishinar ‘Yan sandan ta ce ba a daukar al’amarin a matsayin harin ta’addanci a halin yanzu.

Harin, wanda aka kai a tashar 36th Street a unguwar Sunset Park da ke cike da al’ummomi daban daban ma’aikata a yankin na Brooklyn ya yi sanadin jin raunuka ga mutane 16, wadanda 10 daga cikinsu daga harbin bindiga ne kai tsaye. ‘Yan sanda sun ce biyar daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

((SOURCE: https://www.nbcnewyork.com/news/local/multiple-people-shot-in-brooklyn-subway-sources/3641743/ https://www.dailynews.com/2022/04/12/at-least-5-people-shot-at-new-york-subway-station/