Har Yanzu Ina Cikin Takarar Neman Shugabancin APC-Abdul'aziz Yari

APC

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya ce har yanzu ya na cikin takarar neman shugabancin APC duk da batun tura kujerar arewa ta tsakiya.

ZAMFARA, NIGERIA - Yari wanda ke cewa dimokradiyya dama ce ga kowa ya gwada karbuwar sa, ya bukaci APC ta buda dama a gudanar da zabe yanda ya dace.

Tsohon gwamnan na nuna har yanzu ya na kalubalantar yanda APC ta bar lamuran su ka rikice a Zamfara ta hanyar damka ragamar komai ga gwamna Bello Matawalle da hakan ya zama abun da asalin 'yan jam'iyyar ba za su lamunta ba.

Yari na shan suka daga wasu da ke adawa da yanda ya gudanar da zaben fidda gwani na APC a 2019 da hakan ya sa PDP ta ci bulus daga hukuncin kotun koli.

Ku Duba Wannan Ma Osinbajo Ya Fada Ma Shugaba Buhari Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugabancin Najeriya

Mai takarar shugabancin daga arewa ta tsakiya Mustapha Salihu ya ce ai farar dabara ce yanda jam’iyyar ta raba mukaman ga shiyyoyi don samun kuri’u a babban zabe.

Bayan kammala zaben shugabannin jam’iyya; APC da ma duk jam’iyyu masu niyya za su gudanar da taron zaben dan takarar shugaban kasa a watan mayu.

Abun da ke nuna tura takarar arewa ta tsakiya wani tsari ne na rage ce-ce-ku-ce, shi ne yadda jam'iyyar ta sayarwa Yari takardar tsayawa takarar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Ya Ce Har Yanzu Ya Na Cikin Takarar Neman Shugabancin APC