Har Yanzu Dokar Kare Hakkin Kananan Yara A Najeriya Ba Ta Hana Cin Zarafinsu

Wasu kananan yara

A Najeriya duk da dokokin kare hakkin kananan yara da aka samar a wasu jihohin kasar, masu ruwa da tsaki wajen kare hakkin yara na ci gaba da nuna damuwa akan yadda ake samun matsalolin.

SOKOTO, NIGERIA - Wani babban abin damuwa shi ne yadda wasu ke kokarin hana doka aikinta akan wadanda ake kamawa da hannu a wannan matsalar.

Damuwa da yawaitar cin zarafin kananan yara da ake samu a baya, da kuma fafatukar da kungiyoyi da hukumomi na kasashen duniya suka yi, baya rasa nasaba ga yadda aka samar da dokokin kare hakkin yara a wasu jihohin Najeriya, wadanda tuni gwamnoni sun sanya musu hannu da zummar za su yi aiki yadda ya kamata, kamar a jihar Sakkwato inda gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanya wa dokar hannu a watan Disamban bara.

Ya ce an samar da dokar kare ‘yancin yara ne, don a san ‘yancin yara da kuma muhimmancin basu tarbiya ta kwarai da saka su a tsari na samun ilimi na addini da na zamani da tarbiyya mai kyau. Wannan doka zata kara inganta hakan.

To sai dai wani abu da ke son yin hannun riga da dokokin shi ne har yanzu ana samun matsalolin, kuma ayi ta shawagin kotuna. Kamar misali a Jihar Sakkwato a karamar hukumar Shagari inda aka samu wani matashi da ake tuhumar ya yi wa wata yarinya fyade kuma ya kashe ta.

Jami'in kwamitin sa ido ga wadanda aka ci zarafinsu a yankin Ibrahim Abubakar Jabo ya ce abin ya faru ne lokacin da matashin ya sayi abinci da yarinyar ke sayarwa yaki biyan kudi, da ta yi magana ya ce ta biyo shi ta karba.

Yace bayan dare ya yi har zuwa safe ba'a ga yarinyar ba, amma an san lokacin da yaron ya shiga daji da ita, a karshe dai aka nemo yaron ya nuna inda gawar ta take, aka dauko ta aka je asibitin Shagari aka auna aka tabbatar cewa anyi mata fyade, anyi jana'izar yarinyar tare da daukar hotuna da kwamitin sa ido kan cin zarafin yara ya nemi a yi, yanzu dai batun ya na gaban kotu.

Wani Babban abin damuwa a cewar masu sa idon shi ne yadda ake son hana doka aikinta akan wadanda ake tuhumar.

Rundunar ‘yan sanda a jihohin Sakkwato da Kebbi sun sha nuna wadanda ake tuhuma da cin zarafin yara, bayan gwamnatocin jihohin sun saka hannu ga dokokin, kuma yanzu haka akwai kararraki da yawa a gaban kotuna masu alaka da cin zarafin yara.

Yanzu dai jama'a na ci gaba da zura ido tare da bibiyar kararraki dake gaban kutuna na cin zarafin yara domin ganin yadda za su kaya, abin da zai iya nuna ingancin dokokin da aka samar ko akasin haka.

Saurari rahoton Muhammada Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Har Yanzu Dokar Kare Hakkin Kananan Yara A Najeriya Ba Ta Hana Cin Zarafinsu.mp3