Ana ci gaba da zaman dar-dar a kan iyakar Idomeni, kwana guda bayan da ‘yan sandan Macedonia suka harba yaji mai saka hawaye tare da harba harsashin roba akan daruruwan bakin haure da ke kokarin ketara shingen da aka dasa a yankin Girka.
WASHINGTON, DC —
A yau Litinin, dumbin jama’a sun yi cuncurundo a bangaren iyakar Girka, sai dai babu rahoton da ya nuna cewa an yi wata arangama.
Kungiyoyin jin-kai sun ce kusan mutane 300 aka baiwa magani, bayan arangamar da aka yi jiya Lahadi, mafi yawansu sun samu kulawa ne saboda matsalar numfashi da yajin barkonon tsohuwa ya haddasa, ko kuma raunin da suka ji daga harbin harsashen roba.
A bangaren Macedonia, hukumomin kasar sun ce jami’an tsaro 23 ne suka samu raunuka, mafi yawansu daga ruwan duwatsun da bakin hauren suka musu.
Akalla bakin haure da masu gudun hijra sama da dubu goma, ke makale a kan iyakar Idomeni da ke arewacin kasar Girka tun a tsakiyar watan Fabrairu, bayan da kasashen yankin Balkans suka rufe kan iyakokinsu.