Adeshina ya bayyana hakan ne a cikin makala da ya saba rubutawa a duk mako, inda na cikin wannan mako ya yi marhaba ga kalaman mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya yi ikrarin cewa shugaba Buhari ne dan siyasa mafi farin jini a kasar.
Farfesa Osinbajo dai ya yi wannan kalaman ne a yayin da yake ganawa da jakadu a ofishin jakadnacin Najeriya da ke Birnin Landan na kasar Birtaniya makon jiya.
A cewar Adeshina a tarihin kasar fitattun ’yan siyasar baya da suka yi fafutikar Najeriya ta sami ’yancin cin gashin kan ta wadanda a tarihi ba za’a taba manta su ba kamar su marigaya Malam Aminu Kano, Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo da sauransu, ba su sami irin karbuwa da masu tururruwa wajen ganin shugaba Buhari a duk inda ya je ba.
Karbuwar da shugaba Buhari ke zamu ya zarce tunani a cewar Adeshina.
Saidai ya kara da cewa tsaffin shugabannin Najeriya da suka yi fafutukar samun yancin cin gashin kan kasar bayan shekaru da dama da rasuwarsu ana ci gaba da ganin su da daraja a kasar.
Haka kuma, Adesina ya ce a tsawon shekarun da ya yi da wayau a duniya, ya ga ’yan siyasa da suka hada da marigaya Malam Aminu Kano, Shehu Shagari, Moshood Kashimawo Abiola, Bashir Tofa, Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe, da dai sauransu amma bai taba ganin mai irin farin jinin da shugaba Buhari ya yi ba.
Kusan duk lokacin da shugaban ya kai ziyara wani yanki a cici da wajen kasar, mutane na yin tururruwa wajen sa shi a ido, inji Femi Adesina.
Adeshina ya ce, a duk tafiyar da suka yi a fadin Najeriya da ma wajen kasar shugaba Buhari na da jan hanklin mutane matuka kuma lamarin na bashi mamaki kwarai.
Haka kuma, a cikin rubutun na sa na mako-mako, Adesina ya ce, kwatanta mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mutum amintacce ya na mai cewa maganar shi Osinbajo na da muhimmanci matuka.