Alhaji Kabiru Muhammad dan asalin jihar Naija da ke arewacin Najeriya ya ta fi kasar Saudi Arebiya da nufin gudanar da daya daga cikin rukunan addininsa na Musulunci, wato aikin Hajji a shekarar 2018.
To sai dai Allah bai kaddari zai dawo gida cikin iyalansa ba, domin kuwa ya rasu a birnin Makka, sakamakon makalewa da ya yi a cikin na'urar da ke kai mutane sama, da aka fi sani da lifta.
Wata majiya daga iyalan marigayin ta ce tun a wannan lokaci, hukumar alhazai ta Najeriya tare da gwamnatin jihar Naija, suka yi alkawarin bin kadin hakkinsa, tare da neman a biya iyalansa diyya. Majiyar ta kara da cewa har ma da alkawarin gina wa iyalansa gida.
To sai dai iyalan marigayin sun ce har kawo yanzu ba wani abu da aka yi, hasali ma dai ga baki daya an dain ta da zancen, kamar yadda mai magana da yawun iyalan, Yahaya Abara Idris ya bayyana.
Abara ya ce marigayin ya bar mahaifansa da matan aure biyu da kuma 'ya'ya hudu, alhali kuma shi ne gimshikin gidan, lamarin da ya jefa su cikin wani mawuyacin hali.
A kan haka yayi kira ga hukumomin da ke da alhaki, da su taimaka su nemo wa iyalan hakkin su.
Da wakilin mu ya tuntubi hukumar jin dadin alhazai ta jihar Naija, jami'in hukumar mai kula da yankin Chanchanga, Abu Sufyanu Siri-siri, ya ce lamarin na can tsakanin hukumar alhazan Najeriya da gwamnatin kasar Saudiyya.
A hukumar alhazan Najeriya kuma, kakakin hukumar Fatima Sanda Usara, cewa ta yi tuni da hukumar Hajji da Umara ta kasar Saudiyya ta ci kamfanin da ke kula da na'urar da ta yi sanadiyyar mutuwar Alhaji Kabiru, saboda sakaci da ta yi na kin killace na'urar wadda ta lalace, domin hana mutane su shiga.
Dangane da batun diyyar marigayin, Usara ta ce an yi ta tuntuba tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Saudiyya na neman biyan diyyar, to amma gwamnatin ta Saudiyya ta ce ba ta da ikon sa a biya diyya, sai dai kotu ce kawai ke da wannan ikon.
Ta kara da cewa yanzu haka suna nan suna ci gaba da tattaunawa da lauyoyi domin sanin yadda za'a bullowa al'amarin.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5