Har Yanzu Ba Labarin Fasinjojin Da 'Yan Bindiga Su Ka Sace A Jihar Kogi

Yan bindiga a jihar Sokoto

Jami'an tsaro sun ce har yanzu ba su sami wani bayani ba game da fasinjojin motar safar da 'yan bindiga su ka yi garkuwa da su a jihar Kogi.

Tun a ranar larabar makon jiya ne dai 'yan bindiga su ka yi awon gaba da wadannan fasinjoji da suka fito daga jihar Edo akan hanyarsu ta zuwa Abuja fadar gwamnatin Nigeria a cikin Bus mallakar kamfanin Big Joe Motors,

Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa, ta na kan bincike akan lamarin. A hirar shi da Muryar Amurka, kwamishinan Labarai na jihar kigin Mr.Kencly Fanwo yace suna hada hannu da Jami'an tsaro domin gano abinda ya faru da kuma kokarin kubutar da fasinjojin.

Yace, "Mun kai rahoton lamarin ga Jami'an tsaro anan jihar Kogi kuma sun samu jerin sunayen fasinjojin amma ana kan bincike har ya zuwa yanzu domin tabbatar da an kubutar dasu. Wannan shine dan abinda na samu zuwa yanzu."

Yan bindiga da aka kama

Lokacin da Muryar Amurka ta tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar kogi Mr.William Aya yace, har ya zuwa ranar litanin din nan babu wani ci gaba da suka samu akan lamarin amma dai suna kan Bincike.

Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan bindiga suka yi garkuwa da matafiya a jihar Kogi da ke kan hanyarsu daga wadansu jihohi zuwa birnin tarayya Abuja ba. Ko a watan Fabrairun wannan shekarar, 'yan bindiga sun killace hanya suka tsare motar kamfanin ABC dauke da fasinjoji uku da kuma ta kamfanin God is Good Motors (GIG) guda 12, suka yi amfani da wayar salular daya daga cikin fasinjojin su ka nemi kudin fansa Naira miliyan 15, sai dai babu tabbacin ko an biya kudin fansar kafin sakin dukan fasinjojin bayan kwanaki biyu da garkuwa da su.

Ku Duba Wannan Ma 'Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Sace Mutane 25 A Katsina

'Yan Bindiga sun kuma yi garkuwa da fasinjojin motar jamfanin na GIG (God is Good Motors), a Ore jihar Oyo suna kan hanyarsu zuwa Lagos ranar 13 ga watan Satumba 2018 kafin aka sake su bayan kwanaki 11.

Kamfanin dai ya bayyana cewa, motar tana daukar fasinjoji 13 ne ba 18 ba, kuma basu da tabbacin adadin fasinjojin da ke hannun 'yan bindigar a halin yanzu.

Saurari cikakken rahoton da Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Har Yanzu Ba Labarin Fasinjojin Da 'Yan Bindiga Su Ka Sace A Jihar Kogi