Dan wasan baya na kungiyar Arsenal Hector Bellerin ya ce har yanzu kungiyar ba ta saki kari ba a fafutukar samun gurbi a gasar Zakarun Turai mai zuwa, a yayin da kungiyar ta farfado daga jin jikin da ta yi a farkon dawowa daga hutun annobar coronavirus.
Arsenal din ta sha kashi a wasanninta 2 na gasar Premier na farkon dawowa daga hutun na tsawon watanni 3.
To sai dai gagarumar nasarar da ta samu a ranar Laraba a kan Norwich da ci 4-0, ita ce ta biyu bayan wata nasarar da ta yi a kan Southampton a makon jiya.
Takarar matsayi 4 na saman teburin gasar ta Premier ya kara zafafa bayan da Leicester dake ta uku, da Chelsea da ke ta hudu duk suka sha kashi a jiya, wanda kuma ya rage tazarar maki tsakaninsu da Arsenal, lamarin da ya sa Bellarin ya ke ganin kungiyar na da sauran damar samun shiga gasar zakarun Turai ta badi.
Yanzu haka kuma Arsenal din tana ta 7 ne a saman teburin gasar ta Premier tare da bambancin maki 8 tsakaninta da Chelsea, wacce ta ke matakin karshe na samun shuga gasar Zakarun Turai.