Har Yanzu Ana Kashe Mutane A Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Wani dan rajin kare hakkin bil adama dake jihar Gbaduwe ta kasar Sudan ta Kudu, yace tashe-tashen hankula a gundumar Yambio sai karuwa yake yi.

Ahmed Bashir yace a cikin makonni biyu da suka wuce an kashe a kalla mutane 4 a wajen birninYambio, sai dai kwamishinan ‘yansandan jihar ta Gbaduwe yace an kara inganta matakan tsaro a yankin.

Ahmed Bashir wanda shine shugaban kungiyar kare hakkin bil adama na jihar Gbaduwe yace kashe mutanen da a kayi cikin ‘yan kwanakin ya haifar da tsoro a zukatan mazauna wannan yankin.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai an samu karin yawan kashe-kashe a wannan jihar duk ko da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa tsakanin SOUTH SUDAN NATIONAL LIBERATION MOVEMENT da gwamnatin kasar.

Babban abin damuwa a halin yanzu shine kusan dukkan mazauna wannan wuri suna zaune cikin halin tsoro domin rashin sanin abin daka iya faruwa yanzu ko an jima, da yawan su na cewa menene ke haddasa wannan kashe-kashen kuma su wanene keyin sa.

Ko a cikin farkon wannan watan wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun kashe Rotto Zeni dan shekaru 59 shi da matarsa Antonita Rotto ‘yar shekaru 55. An kuma yi wannan kisan ne a Baakiwiri dake wajen birnin Yambio. Shi dai Rotto Zeni wani sanannen marubuci ne kuma mashahurin malamin makaranta a cikin tsohuwar jihar Equatoria dake yammacin kasar