Har Da Amurkawa Matattu Cikin Wadanda Aka Tura Wa Tallafin COVID-19

Ofishin bincike da sa ido kan harkokin Majalisar Dokokin Amurka da ake kira GAO a takaice mai zaman kansa, ranar Alhamis 25 ga watan Yuni ya bayyana cewa sama da Amurkawa miliyan daya da suka mutu ne aka tura wa jimillar kudi dala biliyan 1.4 a cikin watannin baya-bayan nan, a matsayin kokarin da gwamnati ke yi na tada komadar tattalin arzikin kasar a lokacin da annobar cutar coronavirus ta tsananta.

An tura kudadade lokuta fiye da miliyan 160 da jimullarsu ta kai dala biliyan 269 zuwa ga yawancin Amurkawa, da kuma dala 1,200 da aka hana ba wadanda ke samun kudin shiga sama da dala 98,000 a shekara ko iyali ma'aurata da ke samun dala $198,000 na kudin shiga a shekara.

Duka-duka, kusan kashi 90 cikin 100 na Amurkawa suka samu tallafin kudin, ciki har da dala $500 na yara.

Rahoton na GAO ya ce, an samu sunayen wadanda aka tura wa tallafin ne daga jerin sunayen wadanda suka biya harajin gwamnatin tarayya na shekarar 2018 ko 2019, sai dai gwamnatin kasar ta kasa tsame sunayen wadanda suka mutu.