Bayan murnar cin zaben gwamna da na sauran matai da yawa a jihar Adamawa da ‘yan APC su ka yi, a yanzu an shiga takaddama kan rabon makamai. Rigimar ta fi tsanani ne tsakanin bangaren tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar, masu ganin bangaren nasu ya taka babbar rawa don haka na bukatar kaso mai tsoka, da kuma ‘yan bangaren “mu aka tarar” na Murtala Nyako, wadanda su ke ganin su ne ainihin baraden jam’iyyar.
Alhaji Muhammed Hassan Oscar, wani dan jam’iyyar ta APC ya ce duk wannan rigimar ba a ji ta daga bakin Atiku Abubakar ko bakin Murtala Nyko ba. Ana jin ta ne a bakin masu son shiga gwamnati ko ta halin kaka. Ya ce irin wadannan ‘yan kokarin yin babakere ne ‘su ka kai Nyako su ka baro.’ Ya ce ya kamata a nada mutane bisa irin mukaman da su ka dace da su.
To amma gwamnan jihar mai jiran gado Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla, ya musanta zargin da wasu ke yi cewa zai fifita wani bangare kan wani. Ya ce, “Kowani gida ma na ke, ya zama ada ne, yanzu gida day aba mu da gida biyu; kuma ni wancan gidan da ku ke fadi ban ma san da shi ba.”
Wannan ma na zuwa ne yayin da rikicin yan majalisar dokokin jihar ke kara munana,inda kakakin majalisar Ahmadu Umaru Fintiri ya tsallake rijiya da baya a yunkurin tsige shi da yan majalisar suka sake yi.
Your browser doesn’t support HTML5