Ofishin ‘yan sandan wata karamar hukuma mai suna Franklin a jihar Kentucky dake nan Amurka, sun kafe wata sanarwa a shafin su na Facebook, su na neman duk masu sayar da kwaya da su mika musu takwarorin su.
Gidajen watsa labarai da dama sun fitar da rahotan sanarwar da ‘yan sandan suka yi a yammacin Litinin. Jikin sanarwar a kwai hotan tabar wiwi, kasan ta kuwa akace, “Shin masu takara da ku a kasuwancin ku suna saku asarar kudi? Zamu yi muku maganin su batare da kun biya ko sisi ba!”
Wannan abun dariya ne ace ‘yan sanda suna neman masu laifi ta hanyar sadarwa, amma kasancewar ma’aikatan ‘yan sanda suna tafiya da yadda zamani yake domin gudanar da aikin su na kare da kiyaye mutane.
Shugaban ‘yan sandan Pat Melton yace, sanarwar abin dariya ce, amma ofishin su ba da wasa suke ba.
Idan aka duba kasan sanarwar, an tambayi mutane da su cike wani form akan mai sayar da kwayar da zasu mika, ciki harda sunan sa da irin motar da yake hawa.