Hanyar Da Ta Dace Samari Su Bada Kyauta Ga Masoya -Inji Malam Murtala Yako

A yayin da muka ji ra'ayoyin samari dangane da irin kyautar da tafi dacewa saurayi ya ba budurwa domin kaucewa argin yaudara da kudi wanda yawancin matasan suka amince da shawarar bada kyauta makamanciyar turare, man shafawa da sauran kayayyakin kyaras, a wannan karon mun sami zantawa da wani magidanci ne inda ya bada shawara kamar haka.

Malam Murtala Yako ya fara da cewa lallai kyauta nada tasiri a zamantakewa, kuma dukkan dan adam yakan yaba da duk wani mai kyautata masa kama daga namji zuwa mace.

Sai dai a cewar sa, kyauta tsakanin masoya kamar yadda aka sani a shekarun baya da suka gabata, saurayi yakan aika da duk wata kyautar da zai ba budurwa ne ta hanyar iyayen ta. Ya kara da cewa bai kamata ma ya bada kyautar da hannunsa ba.

Kodashike zamani ya canza, amma al'ada bata canza ba domin kuwa halin kirki abin kauna ne, dan haka yayi kira ga matasa maza da mata da su nisanta kawunan su da kawadayin abin duniya domin samun makomar iyali tagari.

Ga cikakkiyar hirar.