Hankulan 'Yan Nijar Ya Karkata Wajen Taron ECOWAS

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)

Shugabanin kasashen kungiyar ECOWAS za su gudanar da taro a Abuja don tantauna inda zasu bullo wa sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar.

Juyin mulkin da ya haifar da faduwar gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023, wani al’amari da ke fayyace tarkaden dimokradiya a yankin Afrika ta yamma kasancewar ita ce kasa ta 4 renon Faransa a jerin kasashen yankin da suka fada karkashin mulkin soja daga shekarar 2020 kawo yau, dabili kenan ake ganin yiyuwar kungiyar CEDEAO na iya daukan tsauraran matakan da ka iya canza wa Janar Abdourahamane Tchani da mukarrabansa tunani ganin yadda tuni wasu kungiyoyin kasa da kasa suka fara juya wa Majalissar ta CNSP baya.

A hirar shi da Muryar Amurka, Sakataren watsa labaran gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida Souleymane Brah na mai nuna fargaba kan matsalolin da ka iya biyo bayan halin da Nijer ta tsinci kanta a yau.

Janar Abdouramane Tchiani

Lura da hakan ne ya sa shugaban gamayyar kungiyoyin Reseau Esperance Bachar Mahaman ke kiran shugabanin kasashen yammacin Afrika su dauki matakan zakulo hanyoyin rigakafin wannan annoba ta juyin mulki domin a tunaninsa ta hakan ne za a sami dorewar dimokradiya.

A na su bangare sojojin na kokarin shimfida manufofin da suka zo da su a matsayinsu na hukumomin rikon kwarya misalin ganawar da ta hada su da sakatarorin ofisoshin ministoci a yammacin jiya sannan sun kara shigo da wasu Karin sabbin mambobin majalissar ta CNSP.

Sai dai dan rajin kare dimokradiya na kungiyar ROTAB Mahamadou Tchiroma Aissami na cewa ba girin-girin ba.

Nijar

A sanarwar da suka bayar ta kafar gwamnati a yammacin jiya asabar da dare sojojin Majalissar CNSP sun bayyana cewa, sun sami labarin kungiyar CEDEAO na shirin gudanar da taron gaggawa a wannan Lahadi 30 ga watan Yuli a Abuja don tsara farmakin hadin guiwa da wasu kasashen Afrika da nufin mayar da hambararen shugaban kasa kan kujerarsa, suna masu yin kashedi ga dukan wadanda ke neman yi wa Nijer abinda suka kira shishigi a harakokin cikin gidanta.

Yayinda a Yamai tsohon shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya shiga yunkurin samo bakin zaren da ya sarke sakamakon juyin mulkin na 26 ga watan Yuli. A yammacin jiya ya gana da jakadan Faransa da ya dai gefe sojojin da suka kifar da gwamnati haka kuma ya tantauna da jakadun kasashen membobin kungiyar EU.

Zanga zanga bayan juyin mulki

Sai dai kawo yanzu ba a bayyana abinda tuntubar ta bayar ba.

Saurari cikakken rahoton Souley Barmai:

Your browser doesn’t support HTML5

Hankulan 'Yan Nijar Ya Karkata Wajen Taron ECOWAS Na Lahdi 30 Ga Watan Yuli