Uwa ta harbi danta da cuta, ko MTCT a likitance, shine yaduwar kwayar cutar kanjamau daga uwar da ta kamu zuwa ga jaririnta yayin goyon ciki, ko haihuwa, ko kuma shayarwa.
A cewar hukumar yaki da kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS), kimanin mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da kwayar cutar kanjamau a Najeriya kuma uwa ta harbi danta shine hanyar da yara suka fi kamuwa da cutar.
babbar daraktar hukumar yaki da cutar kanjamau ta Najeriya, Dr. Temiope Ilori, tace kasar ta dukufa wajen kawo karshen yaduwar cutar kanjamau a tsakanin jarirai ta hanyar kaddamar da kwamitin sanya idanu a matakin tarayyar kasar.
Wajibi ne mu tallafawa kowa, musamman mata da suka fi rauni wajen kamuwa da cutar kanjamau, da sauran raunana wajen samun kulawar da za ta ceci rayuwarsu sannan su rayu cikin mutunci.
Yara dubu dari da sittin da uku (163, 000) ne ke rayuwa da kwayar cutar kanjamau a Najeriya.
Najeriya ta shafe fiye da shekaru goma tana kokarin rage yaduwar kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri, amma har yanzu kasar na fama da yawaitar afkuwar hakan.
Jami'a mai kula da kungiyar mata masu dauke da cutar kanjamau a Najeriya, Esther Hinchi tace baiwa mata da jariransu tallafi zai hanzarta kawo karshen kwayar cutar kanjamau
“Wannan ne lokacin da ya fi dacewa mu fara neman yadda zamu cike gibin domin tabbatar da cewa yaran dake dauke da kwayar cutar kanjamau na samun kulawar da ta dace. Amma domin cimma wannan buri, muna bukatar tabbatar da cewa iyaye matan, dake karbar magani rabi da rabi sun samu kyakkyawan yanayin da za a basu ayyukan kulawa da tallafi”.
Masana sun bayyana cewa dakile yaduwar kwayar cutar kanjamau na bukatar a samar da kulawar kiwon lafiya ga ilahirin mutanen dake dauke da cutar ko kuma wadanda ke cikin hatsarin kamuwa da ita, musamman wadanda aka kange ko aka mayar saniyar ware a cikin al'umma.
Shugaban asibitin kwararru na Uturu, a jihar Abia, Dr. Ojum Ekeoma Ogwo ya shaidawa Muryar Amurka cewa akwai bukatar dorewar kokarin da ake yi na magance yaduwar kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri tare da raba Najeriya da cutar.
“Yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa da muke kira da NTCT nada yawa kuma har yanzu matsala ce, sai dai muna godiya ga Allah, kuma Najeriya ta samu katafaren ci gaba wajen yawaitar hakan. Abin da ke faruwa shine, duk sa'ilin da aka gano mai ciki na dauke da kwayar cutar ana basu maganin rage karsashin cutar musamman goyon ciki da lokacin haihuwa domin rage yadata ga jariri, wannan shine abin da ke faruwa.
“Zan iya cewa abu ne me yiyuwa a raba Najeriya da kwayar cutar kanjamau. Me yasa nake fadar hakan? Saboda duk da cewa mun yi fama da yawaitar yaduwar cutar a baya, amma yanzu tana raguwa. Mutane na kara fahimtar yadda cutar kanjamau ke yaduwa don haka ake daukar matakan rigakafi tare da bayar da magani.
“Na yi imanin cewa Najeriya, amma kada in cika baki, nan da shekarar 2030 za ta kawar da cutar kanjamau” a cewarsa.
Manufar bikin ranar kanjamau ta duniya ita ce tallafawa kokarin da duniya ke yi na yin rigakafin kamuwa da cutar kanjamau, tare da kara wayar da kai da ilimi game da ita, da tallafawa masu fama da ita ko wadanda ta shafa kai tsaye tare da tunawa da mutanen da cutar ta kashe.