Hamisu Breaker Ya Shiga Sahun Mawakan Najeriya Da Suka Ci Kasuwa A Youtube A 2021

Hamisu Breaker (Instagram/Hamisu Breaker)

Tuni dai Breaker, wanda shi ne mawaki daya tilo daga Arewacin Najeriya da ya samu shiga sahun gaba cikin mawakan, ya wallafa wadannan alkaluma a shafinsa na Instagram.

Fitaccen mawakin Hausa Hamisu Breaker ya shiga jerin mawakan Najeriya da suka ci kasuwa a dandalin Youtube a shekarar 2021 mai karewa.

Dandalin Turntable Charts mai fitar da kididdigar wakokin da aka fi saurare da kallo a shafin na Youtube ne ya fitar da alkaluman.

Cikin jerin mawakan Najeriya da suka hada da mafi akasari na kudu, mawakin na Jaruma ya shiga sahun mawaka nag aba-gaba da aka fi jin wakokinsu.

Alkaluman sun nuna mawakin a saman mawakan kudu irinsu Joe Boy, Patoranking, Yemi Alade, Tekno, Kizz Daniel da sauransu.

Mawaki Davido ne a saman teburin sai Omah Lay a matsayi na biyu sai Wizkid a matsayi na uku.

Tuni dai Breaker, wanda shi ne mawaki daya tilo daga Arewacin Najeriya da ya samu shiga sahun gaba ya wallafa wadannan alkaluma a shafinsa na Instagram.

“Alhamdulillah 2021.” Breaker ya rubuta a kasan alkaluman.