Halin Da Kasuwannin Hannayen Jarin Amurka Ke Ciki

Kasuwannin hannayen jarin Amurka sun sake faduwa warwas a farkon kwatan wannan shekara ta 2020.

Wannan kuma abu ne da kasuwar ba ta taba gani ba.

Kasuwar Dow Jones ta rikito da maki 413, wato kashi 2%, yayin da kasuwar The Standard & Poor’s ma ta yi kasa da maki 2%, sa'anan NASDAQ ta fadi da kashi 1%.

Amma akasarin kasuwannin Turai da Asiya, sun tashi da ‘yar murmurewa.

Radadin da annobar cutar coronavirus ta haddasa a bangaren tattalin arziki, ya sa Dow faduwar kashi 23% tun daga watan Janairu, wato faduwar da ba ta taba yin irinta a kwatan farkon wannan shekara ba a tarihi.

Hakazalika, watan Maris ya kasance wata mafi muni ga kasuwar Dow, tun bayan durkushewar tattalin arzikin Amurka na shekarar 2008.

A yayin da wasu masu lura da al’amura ke cewa kasuwar ta Wall Street ba ta ma kai makurar faduwar da za ta yi ba, wasu kuwa na ganin da zarar cutar coronavirus ta kau, kasuwar za ta zaburo.